A jiya Litinin, 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar shi'a almajiran sheikh Ibrahim Yakubu Elzakzaky da suka fito da jahohin kasar sun gudanar da gagarumar zanga-zanga zuwa gaban ofishin kare hakin bil-adama ta kasar dake birnin Abuja inda suka bukaci kungiyar ta tilastawa gwamnatin kasar ta gudanar da adalci kan wadanda suka harbi marigayyi Sheikh Kasim Umar.
A zanga-zngar neman sakin Shekh Ibrahim Elzakzaky makoni uku da suka gabata da aka yi a birnin Abuja, jami'an 'yan sanda suka halbi marigayi Malam Qasim Umar a tsinyarsa, bayan kwashe makoni biyu yana jiya marigayin ya yi shahada.
Har ila yau mahalarta zanga-zangar sun bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin Sheikh Ibrahim Yakubu Elzakzaky tare da mai dakinsa kamar kotun ta bayar da umarni.